Aya :
1
أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصۡحَٰبِ ٱلۡفِيلِ
Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa* ba?
Aya :
2
أَلَمۡ يَجۡعَلۡ كَيۡدَهُمۡ فِي تَضۡلِيلٖ
Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba?
Aya :
3
وَأَرۡسَلَ عَلَيۡهِمۡ طَيۡرًا أَبَابِيلَ
Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a.
Aya :
4
تَرۡمِيهِم بِحِجَارَةٖ مِّن سِجِّيلٖ
Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta.
Aya :
5
فَجَعَلَهُمۡ كَعَصۡفٖ مَّأۡكُولِۭ
Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye?