ハウサ語対訳 - Abu Bakr Jomy
聖クルアーンの意味の翻訳
アブ・バクル・マフムード・ジョミによる翻訳。ルゥワード翻訳事業センター監修で開発され、意見、評価、継続的な改善のために原文の翻訳が閲覧可能です。
وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيۡتُونِ
Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.[1]
وَطُورِ سِينِينَ
Da Dũr Sĩnĩna.[1]
وَهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٱلۡأَمِينِ
Da wannan gari[1] amintacce.
لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِيٓ أَحۡسَنِ تَقۡوِيمٖ
Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.
ثُمَّ رَدَدۡنَٰهُ أَسۡفَلَ سَٰفِلِينَ
Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni
إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونٖ
Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.
فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعۡدُ بِٱلدِّينِ
To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?
أَلَيۡسَ ٱللَّهُ بِأَحۡكَمِ ٱلۡحَٰكِمِينَ
Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?[1]
share_via