豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。
《古兰经》含义翻译
由阿布·巴克尔·马哈茂德·乔米翻译。在立瓦德翻译中心的监督之下已完成开发,原始翻译可供阅读,以便获取建议、评估和持续发展。
إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ
Idan rãna aka shafe haskenta
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ
Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ
Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ
Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna[1] aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ
Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ
Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ
Kuma idan rãyuka aka haɗa[1] su da jikunkunansu.
وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ
Kuma idan wadda aka turbuɗe[1] ta da rai aka tambaye ta.
بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ
"Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?"
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ
Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ
Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ
Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ
Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ
To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã[1] ba.
ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ
Mãsu gudu suna ɓũya.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ
Da dare idan ya bãyar da bãya.
وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ
Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ
Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ
Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ
Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ
Kuma lalle ne, yã gan shi[1] a cikin sararin sama mabayyani.
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ
Kuma shi, ga gaibi[1] bã mai rowa ba ne.
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ
Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ
Shin, a inã zã ku tafi?
إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ
Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.
share_via