豪萨语翻译 - 艾布·拜克尔·朱米。
《古兰经》含义翻译
由阿布·巴克尔·马哈茂德·乔米翻译。在立瓦德翻译中心的监督之下已完成开发,原始翻译可供阅读,以便获取建议、评估和持续发展。
وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ
Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ
To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare?
ٱلنَّجۡمُ ٱلثَّاقِبُ
Shi ne taurãron nan mai tsananin haske.[1]
إِن كُلُّ نَفۡسٖ لَّمَّا عَلَيۡهَا حَافِظٞ
Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro.
فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ
To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi?
خُلِقَ مِن مَّآءٖ دَافِقٖ
An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna.
يَخۡرُجُ مِنۢ بَيۡنِ ٱلصُّلۡبِ وَٱلتَّرَآئِبِ
Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji.
إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجۡعِهِۦ لَقَادِرٞ
Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne.
يَوۡمَ تُبۡلَى ٱلسَّرَآئِرُ
Rãnar da ake jarrabawar asirai.
فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٖ وَلَا نَاصِرٖ
Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah).
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجۡعِ
Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa.
وَٱلۡأَرۡضِ ذَاتِ ٱلصَّدۡعِ
Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa,[1]
إِنَّهُۥ لَقَوۡلٞ فَصۡلٞ
Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki[1]
وَمَا هُوَ بِٱلۡهَزۡلِ
Kuma shĩ bã bananci[1] bane
إِنَّهُمۡ يَكِيدُونَ كَيۡدٗا
Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai.
وَأَكِيدُ كَيۡدٗا
Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi.
فَمَهِّلِ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَمۡهِلۡهُمۡ رُوَيۡدَۢا
Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu.
share_via