Aya :
1
أَلۡهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ
Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (daga ibada mai amfaninku).
Aya :
2
حَتَّىٰ زُرۡتُمُ ٱلۡمَقَابِرَ
Har kuka ziyarci kaburbura.
Aya :
3
كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
Aya :
4
ثُمَّ كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
Aya :
5
كَلَّا لَوۡ تَعۡلَمُونَ عِلۡمَ ٱلۡيَقِينِ
Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
Aya :
6
لَتَرَوُنَّ ٱلۡجَحِيمَ
Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
Aya :
7
ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيۡنَ ٱلۡيَقِينِ
Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
Aya :
8
ثُمَّ لَتُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ
Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).