Aya :
1
أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ
Shin, ka ga wanda ke ƙaryatãwa game da sakamako?
Aya :
2
فَذَٰلِكَ ٱلَّذِي يَدُعُّ ٱلۡيَتِيمَ
To, wan nan shi ne ke tunkure marãya (daga haƙƙinsa).
Aya :
3
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ
Kuma bã ya kwaaitarwa bisa bãyar da abinci ga matalauci.
Aya :
4
فَوَيۡلٞ لِّلۡمُصَلِّينَ
To, bone yã tabbata ga masallata.
Aya :
5
ٱلَّذِينَ هُمۡ عَن صَلَاتِهِمۡ سَاهُونَ
Waɗan da suke masu shagala daga sallar su.
Aya :
6
ٱلَّذِينَ هُمۡ يُرَآءُونَ
Waɗan da suke yin riya (ga ayyukansu)
Aya :
7
وَيَمۡنَعُونَ ٱلۡمَاعُونَ
Kuma suna hana taimako.