Aya :
20
كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ
A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
Aya :
21
وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ
Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
Aya :
22
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
Aya :
23
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ
Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
Aya :
24
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
Aya :
25
تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ
Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
Aya :
26
كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
Aya :
27
وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ
kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?"
Aya :
28
وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ
Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
Aya :
29
وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
Aya :
30
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ
Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take.
Aya :
31
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ
To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
Aya :
32
وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
Aya :
33
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
Aya :
34
أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ
Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
Aya :
35
ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ
Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
Aya :
36
أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى
Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
Aya :
37
أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ
Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
Aya :
38
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
Aya :
39
فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
Aya :
40
أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ
Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?*