Aya :
19
۞ أَفَمَن يَعۡلَمُ أَنَّمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ ٱلۡحَقُّ كَمَنۡ هُوَ أَعۡمَىٰٓۚ إِنَّمَا يَتَذَكَّرُ أُوْلُواْ ٱلۡأَلۡبَٰبِ
Shin, fa, wanda yake sanin cẽwa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yanã zama kamar wanda yake makãho? Abin sani kawai masu hankali sũ ke yin tunãni.
Aya :
20
ٱلَّذِينَ يُوفُونَ بِعَهۡدِ ٱللَّهِ وَلَا يَنقُضُونَ ٱلۡمِيثَٰقَ
Sũ ne waɗan da suke cikãwa da alkawarin Allah, kuma bã su warware alkawari.
Aya :
21
وَٱلَّذِينَ يَصِلُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيَخۡشَوۡنَ رَبَّهُمۡ وَيَخَافُونَ سُوٓءَ ٱلۡحِسَابِ
Kuma sũ ne waɗan da suke sãdar da abin da Allah Ya yi umurni da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã tsõron Ubangijinsu, kuma sunã tsõron mummũnan bincike.
Aya :
22
وَٱلَّذِينَ صَبَرُواْ ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِمۡ وَأَقَامُواْ ٱلصَّلَوٰةَ وَأَنفَقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ سِرّٗا وَعَلَانِيَةٗ وَيَدۡرَءُونَ بِٱلۡحَسَنَةِ ٱلسَّيِّئَةَ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
Kuma waɗanda suka yi haƙuri dõmin nẽman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma sunã tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan sunã da ãƙibar gida mai kyau.
Aya :
23
جَنَّٰتُ عَدۡنٖ يَدۡخُلُونَهَا وَمَن صَلَحَ مِنۡ ءَابَآئِهِمۡ وَأَزۡوَٰجِهِمۡ وَذُرِّيَّٰتِهِمۡۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يَدۡخُلُونَ عَلَيۡهِم مِّن كُلِّ بَابٖ
Gidãjen Aljannar zama sunã shigarsu, sũ da waɗandasuka kyautatu daga iyãyensu, da mãtansu da zũriyarsu. Kuma malã'iku sunã shiga zuwa gunsu ta kõwace kõfa.
Aya :
24
سَلَٰمٌ عَلَيۡكُم بِمَا صَبَرۡتُمۡۚ فَنِعۡمَ عُقۡبَى ٱلدَّارِ
"Aminci* ya tabbata a kanku sabõda abin da kuka yi wa haƙuri. Sãbõda haka madalla da ni'imar ãƙibar gida."
Aya :
25
وَٱلَّذِينَ يَنقُضُونَ عَهۡدَ ٱللَّهِ مِنۢ بَعۡدِ مِيثَٰقِهِۦ وَيَقۡطَعُونَ مَآ أَمَرَ ٱللَّهُ بِهِۦٓ أَن يُوصَلَ وَيُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمُ ٱللَّعۡنَةُ وَلَهُمۡ سُوٓءُ ٱلدَّارِ
Kuma waɗanda* suka warware alkawarin Allah daga bãyan ƙulla shi, kuma sunã yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi dõmin a sãdar da shi kuma sunã ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan sunã da wata la'ana, kuma sunã da mũnin gida.
Aya :
26
ٱللَّهُ يَبۡسُطُ ٱلرِّزۡقَ لِمَن يَشَآءُ وَيَقۡدِرُۚ وَفَرِحُواْ بِٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَمَا ٱلۡحَيَوٰةُ ٱلدُّنۡيَا فِي ٱلۡأٓخِرَةِ إِلَّا مَتَٰعٞ
Allah ne Yake* shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuntatãwa. Kuma sun yi farin ciki da rãyuwar dũniya, alhalikuwa rãyuwar dũniya ba ta zama ba dangane ga ta Lãhira fãce jin dãɗi kaɗan.
Aya :
27
وَيَقُولُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَوۡلَآ أُنزِلَ عَلَيۡهِ ءَايَةٞ مِّن رَّبِّهِۦۚ قُلۡ إِنَّ ٱللَّهَ يُضِلُّ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِيٓ إِلَيۡهِ مَنۡ أَنَابَ
Kuma wanɗanda suka kãfirta, sunã cẽwa, "Don me ba a saukar da wata ãyã ba a kansa daga Ubangijinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Yanã ɓatar da wanda Yake so kuma Yanã shiryar da wanda ya tũba zuwa gare shi."
Aya :
28
ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَطۡمَئِنُّ قُلُوبُهُم بِذِكۡرِ ٱللَّهِۗ أَلَا بِذِكۡرِ ٱللَّهِ تَطۡمَئِنُّ ٱلۡقُلُوبُ
Waɗanda suka yi ĩmãni kuma zukãtansu sukan natsu da ambaton Allah. To, da ambaton Allah* zukãta suke natsuwa.