Aya :
1
إِنَّا فَتَحۡنَا لَكَ فَتۡحٗا مُّبِينٗا
Lalle Mũ, Mun yi maka rinjãye (a kan maƙiyanka), rinjaye bayyananne.
Aya :
2
لِّيَغۡفِرَ لَكَ ٱللَّهُ مَا تَقَدَّمَ مِن ذَنۢبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ وَيُتِمَّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَيۡكَ وَيَهۡدِيَكَ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا
Dõmin Allah Ya shãfe abin da ya gabãta na laifinka* da abin da ya jinkirta, kuma Ya cika ni'imar Sa a kanka, kuma Ya shiryar da kai ga hanya madaidaiciya.
Aya :
3
وَيَنصُرَكَ ٱللَّهُ نَصۡرًا عَزِيزًا
Kuma Allah Ya taimake ka, taimako mabuwãyi.
Aya :
4
هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنزَلَ ٱلسَّكِينَةَ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ لِيَزۡدَادُوٓاْ إِيمَٰنٗا مَّعَ إِيمَٰنِهِمۡۗ وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَلِيمًا حَكِيمٗا
Shĩ ne wanda Ya saukar da natsuwa a cikin zukãtan mũminai dõmin su ƙãra wani ĩmãni tãre da imãninsu, alhãli kuwa rundunõnin sammai da ƙasa, na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima.
Aya :
5
لِّيُدۡخِلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَا وَيُكَفِّرَ عَنۡهُمۡ سَيِّـَٔاتِهِمۡۚ وَكَانَ ذَٰلِكَ عِندَ ٱللَّهِ فَوۡزًا عَظِيمٗا
Dõmin Ya shigar da mũminai maza da mũminai mãtã gidãjen Aljanna, kõgunan ruwa na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen, sunã madawwama a cikinsu kuma Ya kankare musu mũnãnan ayyukansu. wannan abu ya kasance a wurin Allah babban rabo, mai gimia.
Aya :
6
وَيُعَذِّبَ ٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱلۡمُنَٰفِقَٰتِ وَٱلۡمُشۡرِكِينَ وَٱلۡمُشۡرِكَٰتِ ٱلظَّآنِّينَ بِٱللَّهِ ظَنَّ ٱلسَّوۡءِۚ عَلَيۡهِمۡ دَآئِرَةُ ٱلسَّوۡءِۖ وَغَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِمۡ وَلَعَنَهُمۡ وَأَعَدَّ لَهُمۡ جَهَنَّمَۖ وَسَآءَتۡ مَصِيرٗا
Kuma Ya yi azãba ga munãfikai maza da munãfikai mãtã da mushirikai maza da musbirikai mãtã, mãsu zaton mugun zato game da Allah, mugunyar masĩfa mai kẽwayẽwa ta tabbata a kansu, kuma Allah Ya yi hushi da su, kuma Ya la'ane su, kuma Ya yi musu tattlain Jahannama kuma ta mũnana ta zama makõma (gare su).
Aya :
7
وَلِلَّهِ جُنُودُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا
Rundunõnin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
Aya :
8
إِنَّآ أَرۡسَلۡنَٰكَ شَٰهِدٗا وَمُبَشِّرٗا وَنَذِيرٗا
Lalle Mũ Mun aike ka, kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi.
Aya :
9
لِّتُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦ وَتُعَزِّرُوهُ وَتُوَقِّرُوهُۚ وَتُسَبِّحُوهُ بُكۡرَةٗ وَأَصِيلًا
Dõmin ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) sãfiya da maraice.